Aminu Abdullahi Ibrahim
Hukumar Ilimin Bai daya ta jihar Kano (SUBEB) ta ce fiye da mutum dubu 16 ne suka nemi aikin koyarwa na shirin gwamnatin Kano da zata dauki karin malaman makaranta dubu 4.
Daraktan sadarwa na hukumar Balarabe Danlami Jazuli, ne ya bayyana hakan a tattaunawarsa da Premier Radio.
Wannan na zuwa ne bayan da gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya bayar da umarnin kara daukar malaman makarantun Firamare da karamar Sakandire.
Balarabe Danlami Jazuli, ya ce za a fara rubuta jarabawar ne a ranar Uku ga watan Janairu da muke ciki a cibiyoyin da aka tanadar da suka hada da Kwalejin Noma ta Audu Bako dake Dambatta da Rabiu Kwankwaso College Of Remidial Studies dake Tudun Wada.
Sauran guraren sune FCE dake Bichi da cibiyar kwamfuta dake sakatariyar Audu Bako da Jam’ar Aliko Dangote dake Wudil.
Ya ce za ayi jarabawar ne a Kwamfuta a don haka ya gargadi wadanda babu sunansu da su kaucewa guraren da aka tanadar.
Danlami Jazuli, ya ce an samar da yanayi mai kyau ta yadda za a dauki wadanda suka cancanta kuma suka yi nasara a jarabawar da aka shirya.
Ya kuma bukaci malaman da zasu rubuta jarabawar da su je guraren cikin tsari da kuma shedar rubuta jarabawa.
