
Tawagar lauyoyin ɗan kasuwa, Abdullahi Bashir Haske, ta zargi Hukumar Yaƙi da Yi wa Tattalin Arziki Ta’annati ta EFCC da saɓawa doka wajen ayyana cewa tana neman shi ruwa a jallo kan zargin haɗin baki da almundahanar kuɗaɗe.
A wata sanarwa da jagoran lauyoyin, Barista Nkemakolam Okoro, ya fitar, ya bayyana matakin a matsayin wuce gona da iri a ayyukan hukumar.
Ya ce akwai ƙarar da ke gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja wadda ke kalubalantar hukumar kan ingancin takardar izinin kama ɗan kasuwar kuma ɗan sirikin jagoran adawa Atiku Abubakar.
Okoro ya ce sun yi mamaki da matakin EFCC saboda a bayanan kotu, Abdullahi Haske ya nuna cikakken haɗin kai ga hukumar tun da farko, inda ya amsa gayyata a watan Yuli, ya kuma mika duk wasu takardun da ake buƙata, ciki har da na lafiyarsa bayan ya fuskanci rashin lafiya a lokacin da ta tsare shi.
Ana dai ganin matakin EFCC ɗin na da alaka da siyasa da kuma rashin jituwar da ke tsakanin Bashir Haske da shugaban hukumar Ola Olukayode.
Sai dai EFCC ta musanta wannan zargi tana mai cewa ba ta kama shi saboda alaƙarsa da Atiku ba.
A tattaunawarsa da Daily Trust, kakakin hukumar, Dele Oyewale ya ce tin a shekarun baya ake tuhumarsa kuma aka bayar da shi beli.
Sai dai rundunar ƴansanda ta ƙasa da ƙasa ta yi watsi da matakin EFCC na ayyana Abdullahi Haske ruwa a jallo.
INTERPOL a wasiƙar da ta aikewa jaridar People Gazette, ta ce tana aiki ne da umarni idan bai take haƙƙin mutum ba.