Shugaban jam’iyyar NNPP na jihar Kano, Hashimu Dungurawa, ya yi martani kan jita-jitar da ake yaɗawa kan tsohon gwamnan jihar nan Rabiu Musa Kwankwaso game da batun komawarsa kungiyar hadakar jam’iyyun adawa ta ADC.
Dungurawa ya musanta cewa Kwankwaso ya shirya tattara kayansa domin komawa jam’iyyar hadaka ta ADC, Shugaban na NNPP ya bayyana Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da cewa ba shi daga cikin ƴan siyasar da za su yanke hukunci ba tare da cikakken nazari ba.
Jaridar Punch ta rawaito cewa Hashimu Dungurawa ya bayyana hakan ne lokacin da yake magana da manema labarai.
Yayin da yake tsokaci kan wasu da ake cewa mabiyansa ne da ke nuna damuwa da yadda tafiyar siyasar sa, ya ce magoya bayan Kwankwaso ba su da shakku kan jagoran nasu.
Yayin da yake bayani kan jita-jitar cewa an ga Kwankwaso yana ganawa da wasu ƴan siyasa daga wasu jam’iyyu, Dungurawa ya ce, Kwankwaso jajirtaccen dan siyasa ne mai dauke da kwarewa, dan haka ba zai boye kansa ko ya ware daga wasu mutane ba.
