Shugaban Karamar Hukumar Sumaila da sauran manyan jami'an gwamnanti a yayin bikin karbar yaran 59 a harabar ma'aikatar a Kano
Gwamnatin Kano za ta ba yaran da Allah Ya yi masu baiwa ta kulawa ta musamman ta hanyar ba su horo a fannin kimiyya da fasaha
Kwamishinan ilimi na jihar, Dakta Ali Haruna Makoda ne ya bayyana hakan, lokacin da ya ke sanya idanu kan jarrabawa ta musamman da aka shiryawa daliban a makarantarsu da ke garin Ganduje.
“Gwamnati za ta zurfafa bincike domin ci gaba da gano yara ‘yan baiwa a jihar tare da ba su horo ta yadda za su yi gogayya da takwarorin su a fannin kimiyya da Fasaha a Najeriya da duniya baki daya.
- Majalisar dokokin kano ta ce zata dafawa yunkurin gwamnati na bunkasa fannin ilimi.
- Gwamnatin Kano ta ware miliyan 242 domin gyara makarantar Government Technical Danbatta.
“Makarantar ta maza zalla wadda da Gwamna Abba Kabir Yusif ya samar za ta fara aiki ne a watan Janairun sabuwar shekara za ta yi aiki da manufar rainon baiwa ta musamman da Allah ya yiwa wasu daga cikin yaran Kano a fannoni daban-daban na kimiyya da fasaha”. In ji shi.
Kwamishinan ya fadi hakan ne ta bakin Daraktan Dubawa Da Tantance Ayyuka Na Ma’aikatar Ilimi, Auwal Mustapha Muhammad da ya wakilce shi a taron.
Makarantar wadda aka yiwa suna da Kano Gifted Academy, babbar sakandire ce, kuma kyauta ga duk dalibin da ya samu nasarar jarrabawar shiga.
Daliban za su fara karatu daga ne a SS1 a watan janairun 2026.
