Gwamnatin tarayya za ta binciki musabbabin dawo da satar dalibai a kasar nan bayan tsawon shekaru da daina yin hakan.
Ministan tsaro Muhammad Badaru Abubakar ne ya bayyana hakan a hirarsa da BBC a ranar Laraba.
Badaru ya ce, hakan zai taimakawa ma’aikata tunkarar kalulaban matsalar rashin tsaro a kasar nan.
“Sakamakon binciken zai ba wa makarantu kariya, zai kuma ci gaba da guduna a fadin kasar nan domin dakile duk wani hari da yan ta’addar za su kawo makarantun da kuma yinkurin sace daliban”. In ji shi.
Ministan ya ce ‘yan ta’addar da suke kaiwa al’umma hare-hare suna satar hanya ne domin gudunar da dukkanin abuna suke da bukata.
