
Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya, ta Majalisar Dinkin Duniya WHO ta ce, hawan jini na kashe mutum miliyan 10 a kowace shekara, cutar na kuma hallaka kimanin mutune biliyan ɗaya da rabi a duniya
Bayanin hakan na kunshe ne cikin wani rahoto da rukumar ta gabatar kan matsalar hawan jini a babban taron Majalisar Dinkin Duniya da ake gudarwa a birnin New York ta Amurka
“Fiye da mutum 1,000 ne ke mutuwa a kocewa sa’a sakamakon bugun zuciya da mutuwar ɓarin jiki, waɗanda dukkaninsu hawan jini ke haifar da su.” In ji shugaban hukumar Tedros Adhanom Ghebreyesus.
Ya kuma kara da cewa, akwai buƙatar ƙasashe su tashi tsaye domin ɗaukar matakan daƙile barazanar hawan jini domin ceto rayukan al’ummar duniya.
- WHO Ta Ce Babu Motocinta da Aka Bari Su Shiga Gaza
- Majalisar dinkin duniya ta kudiri aniyar tallafawa gwamnatin Kano a bangarori da dama.
“Hawan jini ne babban abin da ke haifar da bugun zuciya da ciwon koda da kuma mutuwar ɓarin jiki – waɗanda ta ce dukkaninsu ana iya magance su”, in ji shi.
Shugaban ya kuma ce, mutum biliyan 1.4 ne ke fama da hawan jini a duniya a shekarar 2024, kuma a cewar rahoton kashi ɗaya ne cikin biyar aka iya magancewa ta hanyar magani da kuma bin matakan da suka dace na lafiya.
Ya kuma kara da cewa, hawan jini na kashe mutum miliyan 10 a kowace shekara, duk da cewa ana iya magance shi.
Hukumar lafiyar ta yi nazari ne a ƙasashe 195, kuma ƙananan ƙasashe ne galibi matsalar ta fi kamari.
Sannan ta kuma ce, idan har hukumomi ba su ɗauki mataki ba, to miliyoyin mutane za su ci gaba da mutuwa ba shiri, wanda zai iya shafar tattalin arzikin ƙasashen duniya.
