Shugaban jam’iyyar NNPP na Jihar Kano, Hashimu Sulaiman Dungurawa, ya bayyana yadda APC ke bukatar Kwankwaso a tafiyarsu.
Domin jam’iyyar ba ta da ƙarfin da zai kai ta ga samun nasara a 2027, sai da shi.
Shugaban ya fadi hakan ne yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a sakatariyar jamiyyar na jihar.
- Muna Tare Da Kwankwaso A NNPP – ‘Yan Majalisar Wakilai 13
- Ba Tinubu ne ya sauko da farashin kayan abinci ba – ADC
“APC a Kano har ma da matakin ƙasa ta rasa shugabanci da tsari, wanda hakan ta jam’iyyar ke yawan neman kusanci da Kwankwaso.
“Wannan mutanen APC ba su da ƙarfi, kuma a halin yanzu sun shiga ruɗani. Sun san cewa idan babu Kwankwaso, ba za su iya cin zaɓe a 2027 ba”. In ji shi.
Dungurawa ya kafa hujja da cewa dalilin hakan ta sa APC ta ke yawan zawarcinsa domin tattauna wa.
Amma hankalin jagoran nasu na kan talakawa da jin dadin ‘yan Najeriya.
A yayin taron shugaban ya jam’iyyar ya tabo wasu batutuwa na siyasa da ya shafi jiha da Kuma Kasa baki daya.
