
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar ya ce, Shugaba Bola Tinubu ba ya bayara da jagoranci na gari wajen magance matsalar tsaro a Nijeriya.
Atiku ya faɗi haka ne lokacin da ya gana da wasu shugabannin siyasa daga Jihar Borno ƙarƙashin jagorancin Mohammed Kumalia.
“yan bindiga da ’yan ta’adda na ci gaba da mamaye ƙauyuka tare da hana manoma yin noma, hakan a babbar gazawar shugabanci ne.
“Taɓarɓarewar tsaro a yankunan Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma da kuma Arewa ta Tsakiya na nuna cewa gwamnati ba ta yin abin da ya dace don kare rayukan jama’a ba”. In ji shi.
Atiku ya kuma jaddada cewa dakarun tsaron Nijeriya suna da ƙarfin da za su iya fatattakar ’yan ta’adda, amma abin da ya rage shi ne samun ingantaccen shugabanci da ƙwarin gwiwa daga fadar shugaban ƙasa.
Sannnan Atiku ya yi kira ga ’yan Nijeriya da su haɗa kai domin ceto ƙasar nan, inda ya bayyana cewa dawo da zaman lafiya da bunƙasa tattalin arziƙi ya kamata su zama fifiko.