Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Najeriya, INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya bayyana cewa yana yawan samun saƙonnin barazanar kisa sakamakon aikin da yake gudanarwa.
Amupitan ya bayyana hakan ne yayin wani taron shawarwari da hukumar ta gudanar tare da kwamishinonin zaɓe na jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya, Abuja.
Ya ce gudanar da zaɓe aiki ne da ke tattare da matsin lamba da suka daga ɓangarori daban-daban, duk da ƙoƙarin da jami’an hukumar ke yi na sauke nauyin da aka ɗora musu.
Shugaban hukumar ya bayyana damuwarsa kan barazanar da jami’an zaɓe ke fuskanta, musamman yayin da ake tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.
Ya kuma gargaɗi kwamishinonin zaɓe da su guji sakaci ko duk wani abu da zai iya kawo cikas ga gudanar da sahihin zaɓe.
Farfesa Amupitan ya jaddada muhimmancin gudanar da ayyukan hukumar bisa gaskiya, adalci da bin dokokin zaɓe, domin ƙarfafa amincewar jama’a da tsarin zaɓen ƙasar.
Sai dai bai bayyana waɗanda ake zargin suna aika masa da saƙonnin barazanar ba, ko matakin da hukumomin tsaro suka ɗauka kan lamarin.
