Asusun tallafawa kananan yar na majalisar dinkin duniya UNICEF ya yabawa gwamnatin jihar Kano bisa yadda ta zama ta farko cikin jihohin Najeriya, wajen bayar da gudunmawar kudi har naira milyan 500 don amfani da su wajen bunkasa shirin samar da abinci mai gina jiki ga kananan yara a fadin jihar.
Jami’in dake kula da shirin anan Kano Mr Rahama Farah ne ya bayyana hakan a ranar Talata, yayin taron masu ruwa da tsaki da suka gudanar kan yadda za a bunkasa kula da lafiyar kananan yara, da kuma kawo karshen kalubalen da suke fuskanta yayin tasowa.
Ganin gudunmawar da gwamnatin ta bayar ya sanya asusun shima ya kara makamancin kudin don sakawa cikin asusun da akan yi amfani da kudin wajen yaki da matsalar rashin abinci mara gina jiki ga yaran, yana mai cewa karkashin asusun suna fatan yaray an watanni 6 zuwa 59 a kalla milyan 2.6 su amfana, yayin da suma iyaye mata masu dauke da juna biyu dubu dari 5 ake fatan su ci gajiyar tallafin.
