Kungiyar Tuntuba ta Arewa (ACF) za ta gudanar da bikin cika shekaru 25 da kafuwarta daga ranar Alhamis, 20 zuwa Asabar, 22 ga Nuwamba a jihar Kaduna.
An kafa ACF a shekarar 2000 domin inganta haɗin kai, zaman lafiya da cigaba a Arewa, tare da tabbatar da cewa yankin na taka muhimmiyar rawa a harkokin ƙasa.
A yayin bikin, ana sa ran Alhaji Aliko Dangote zai gabatar da jawabi, sannan za a karɓi saƙonnin taya murna daga Shugaba Bola Tinubu, fitattun dattawan Arewa da shugabanni daga Kudancin Najeriya.
Bugu da ƙari, za a kaddamar da asusun tallafin Naira biliyan 100 domin tallafawa ayyukan raya al’umma a matakin ƙasa.
