Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta bayyana alhini da jimami kan rasuwar wasu maniyyata biyu da ske shirin zuwa aikin Hajjin bana, bayan sun gamu da mummunan hadarin mota.
Mamatan sun hada da Alƙasim Ibrahim Walawa mai shekaru 48 da mahaifiyarsa, Hajiya Hadiza Garba mai shekaru 73.
Lamarin ya faru ne a kan hanyar Rimin Gado zuwa cikin birnin Kano, inda aka ce hadarin ya yi sanadiyyar rasuwar su nan take.
Rahotanni sun ce marigayin Alƙasim ya bar mata biyu da ‘ya’ya bakwai, yayin da Hajiya Hadiza ta rasu ta bar ‘ya’ya biyar.
Dukkansu ‘yan asalin ƙauyen Walawa ne da ke ƙaramar hukumar Kabo a jihar Kano.
Hukumar ta bayyana rasuwar a matsayin abin tausayi matuƙa, musamman ganin cewa mamatan na kan hanyarsu ta zuwa ƙasa mai tsarki domin sauke farali.
A cikin sakon ta’aziyya mai dauke da sa hannun mai magana da yawunta, Suleiman A. Dederi, hukumar ta yi addu’ar Allah Ya gafarta musu.
“Mun yi matuƙar jimami da wannan rashi. Muna roƙon Allah Ya jikansu da rahama, Ya kuma bai wa iyalansu haƙuri da juriya,” in ji sanarwar.
Hukumar ta kuma miƙa sakon ta’aziyya ga iyalan mamatan, tana addu’ar Allah Ya ba su ƙarfin zuciya a wannan lokaci na alhini.
