Ƙungiyar ma’aikatan jinya da ungozoma ta kasa reshen jihar Zamfara ta sanar da shiga yajin aiki na kwana shida a matsayin na gargaɗi.
Shugaban ƙungiyar Malam Sani Shehu ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da kungiyar ta gudunar, ya ce sun ɗauki wannan matakin ne domin jawo hankalin gwamnatin jihar kan sabon tsarin albashinsu.
Ya ce duk da gwamnatin ta amince da sabon tsarin albashi na na ma’aikatan lafiya amma ta ƙi aiwatar da tsarin albashin likitoci.
Hakazalika matakin nasu zuwa ne bayan ƙungiyar ta yi yajin aikin gargaɗi na kwana bakwai daga 11 ga watan Satumba, wanda aka dakatar shi bayan kwana ɗaya saboda alƙawarin da gwamnati ta yi musu.
Shugaban ƙungiyar Malam Sani Shehu ya kara da cewa za su ci gaba da gudunar da yajin aikin tun daga yau daga Asabar zuwa Talata mai zuwa.
Ya kuma tabbatar da cewa, kofar kungiyar a bude take a koda yaushe domin tattaunawa da bangaran gwamnatin jihar ganin sun dakatar da yajin aikin.