
Ƙungiyar agaji ta Red Cross ta ce ta dakatar da ayyukanta a Zirin Gaza saboda ƙaruwar hare-haren sojojin Isra’ila a ƙwayar birnin.
Red cros ta ce, dubban Falasɗinawa na cikin wani mawuyacin hali, yayin ake ci gaba da yi musu ruwan bama-bamai.
Rahotonni daga birnin sun ce a aƙalla Falasɗinawa 41 aka kashe a yau Laraba a yankin, mafi yawansu a birnin Gaza.
Rundunar sojin Isra’ila ta fitar da sabon umurnin da ya buƙaci mazauna birnin su fice zuwa kudancin Gaza.
Ministan tsaron Isra’ila, Isrea Katz ya ce manufar farmakin ita ce ƙarfafa ƙawanyar da suka yi wa mayaƙan Hamas a Gaza.
Kawo yanzu shugabanin Hamas ba su mayar da martani ga shirin shugaba Trump na kawo ƙarshen yaƙin ba.