
Haɗaka Malaman Ahlussunna na jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Dakta Abdallah Gadon Kaya suma sun kai nasu Korafin a matsayin martani ga zargin batanci da ake yiwa Malam Lawan na Masallacin Triumph.
Dakta Gadon Kaya ne ya bayyana haka a wani bidiyo a maraicen ranar Alhamis a kofar ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar bayan mika takardar.
“Mun zo nan ne don mika tamu takardar koken ga Sakataren Gwamnatin Jihar Kano kamar yadda gwamna Jihar Kano ya ba da umarni ga ‘yan zanga-zanga.
“Mu ba zanga-zanga muke yi ba, ba ma kuma zanga-zanga, mun kawo takardar kamar yadda suma ka kawo…” In ji Malamin.
Sheihun Malamin, kamar yadda bidiyon ya nuna, ya samu rakiyar dinbin mabiya, ya kuma ce ba su samu Sakataren Gwamnatin ba, amma sun mika takarda, kuma an karba. Kuma suna jiran kira a duk lokacin da aka kira sauran wadanda suka fara shigar da korafin da a zo a zauna a tattauna lamarin.
Wasu masu zanga-zanga a jihar sun yi zargin Malam Lawan limamin Masallacin Triumph da yin kakkausar lafazi kan Manzon Allah Tsira da Amincin Allah su Tabbatar a gare shi, inda suka nemi gwamnatin Jihar da ta dau mataki.