
Hukumar kula da aikin hajji ta Kasa NAHCON ta ce hukumomin Saudiyya sun bayyana cewa ba za a ƙara wa’adin biyan kuɗi, ɗa kuma sauran shirye-shirye na aikin hajjin 2026 ba.
Shugaban hukumar, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya bayyana hakan a taron da aka yi da kamfanonin da ke da lasisin gudanar da aikin hajji, inda ya jaddada muhimmancin bin jadawalin da Saudiyya ta gabatar.
Kwamishinan ayyuka na hukumar, Prince Anofiu Elegushi, ya gargadi masu kokarin zuwa da su guji jinkiri, inda ya ce a wannan lokacin idan aka rufe an rufe kenan babu karin lokaci.
Ya ce a bara wasu kamfanoni sun yi sakaci da tsammanin za a ƙara wa’adi, abin da ya sa suka rasa damar zuwa, lamarin da ya zama babban darasi domin hajjin bana.