U.S. President Donald Trump looks on as he meets with the White House Task Force on the FIFA World Cup 2026 in the Oval Office at the White House in Washington, D.C., U.S., November 17, 2025. REUTERS/Evelyn Hockstein
Shugaban Amurka Donald Trump ranar Jumma’a ya ce yana duba yiwuwar kammala” hare-haren soji da ake kai wa Iran sannan ya ƙara da cewa sauran ƙasashe ne suka kamata su “bayar da kariya tare da sanya ido” kan Mashigin Hormuz saboda muhimmancinsa.
Trump a wani saƙo da ya wallafa a shafin sada zumunta na Truth Social yace sun kusa cim ma muradunsu don haka suna duba yiwuwar kammala harin da suke yi akan Iran.
Lamura sun dagule a yankin Gabas ta Tsakiya tun bayan da Amurka da Isra’ila suka ƙaddamar da hare-hare a Iran ranar 28 ga Fabrairu. Rahotanni sun ce hare-haren sun kashe aƙalla mutum 1,300, cikinsu har da ƙananan yara mata ‘yan makarantar firamare fiye da 150.
Iran ta mayar da martani ta hanyar harba makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa kan Isra’ila da kuma kayayyakin Amurka da ke ƙasashen Larabawa, abin da ya ƙara yamutsa yaƙin.
