Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana damuwarta kan kama tsohon shugaban Hukumar Karɓar Korafe-Korafe da Yaki da Cin Hanci ta jihar (PCACC) Muhuyi Magaji Rimin Gado, da Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta yi.
Gwamnatin ta kuma nemi rundunar da ta gaggauta sakinsa tare da neman afuwarsa kan kamun da aka yi masa.
Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano Abdulkarim Kabir Maude SAN ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da ya gabatar a daren Junma’a.
Kwamishinan ya zargi cewa kamun da aka yi wa Muhuyi Magaji na da alaƙa da da binciken da ya soma gudanarwa kan tsohuwar gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje, inda maʼaikatar shariʼa ta sahale masa ci gaba da bin lamarin a halin yanzu.
“An kama Rimin Gado ne a ofishin sa da ke kan titin Zaria Road Kano ba tare da takardar shedar kamu ba ta (warrant) sannan daga bisani aka kai shi hedikwatar ’Yansanda da ke Bompai, wanda daga nan kuma aka tafi da shi zuwa Abuja.
“Mun tuntuɓi rundunar ƴan sanda kan lamarin, amma babu cikakken bayani, kuma haka ƴan sandan da suka tafi da shi ba su sanar da shi bayanin komai ko makusanta ko iyalansa ba”. In ji shi
Gwamnatin jihar ta nuna rashin jin daɗi kan yadda aka yi kaman da kuma lokacin da aka zaba, ta kuma bukaci a sako shi da cikin gaggawa da kuma neman afuwarsa daga rundunar.
