Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ƙaddamar da rabon fom ɗin JAMB guda 10,000 kyauta ga daliban makarantun sakandare a faɗin jihar Kano.
A lokacin kaddamar da shirin da aka gudanar a wani biki na musamman, kwamishinan ilimi na Kano, Ali Haruna Makoda, wanda ya wakilci gwamnan, ya ce wannan mataki wani ɓangare ne na manufofin gwamnati na tallafawa ɗalibai da ƙarfafa ilimi a matakin sakandare da na gaba.
Baya ga rabon fom ɗin JAMB, gwamnatin ta kuma ƙaddamar da wani shirin horar da ɗaliban 10,000 da suka ci gajiyar tallafin kan yadda ake amfani da tsarin jarrabawar ta na’ura mai kwakwalwa, wanda za a gudanar a cibiyoyi daban-daban da aka ware a sassan jihar.
Mashawarcin gwamna kan harkokin ilimi, Tajuddin Gambo, ya bayyana cewa gwamnatin jihar za ta samar da sufuri kyauta ga dukkan daliban da za su halarci horon, tare da jaddada muhimmancin dagewa wajen shiryawa domin cin jarrabawar.
Ya ƙara da cewa gwamnatin Kano na da niyyar taimaka wa waɗanda suka yi nasara wajen zaɓin makarantu mafi inganci domin ci gaba da karatunsu a matakin gaba da sakandare.
Ɗaya daga cikin waɗanda suka ci gajiyar shirin, Fatima Mukhtar Umar, ta nuna farin cikinta tare da godewa Gwamna Abba Kabir Yusuf, tana mai alwashin cewa ba za ta sa gwamnati ta yi nadamar zaben ta ba.
