
Ministan Lantarki Adebayo Adelabu ya ce gwamnatin tarayya na nazarin sake ƙarin kuɗin lantarki.
Adelabu ya ce za yi Karin ne domin cike giɓin bashin naira tiriliyan huɗu da ake bin masana’antar.
Ministan ya fadi hakan ne a wani taron masu ruwa da tsaki a Abuja.
Ya kuma ce, ta wannan hanya kaɗai za a iya ceto masana’antar da kuma cigaba da gudanar da ayyukanta.
Duk da karin ƙudin lantarki da aka yi wa kwastamomi da ke tsarin Band A, ‘yan Najeriyar na kokawa ganin cewa wutar ba ta waɗatar da su.
Amma Adelabu ya ce matakin na da muhimmanci wajen inganta tattalin arziki da cigaban ƙasar.
Wannan dai na nufin gwamnatin za ta kawo ƙarshen tsarin tallafin da ake bai wa ɓangaren lantarki, yanayin da zai tilasta ƙarin kuɗin wuta ga kowa.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa a watannin shida na farkon wannan shekarar gwamnati ta biya tallafin naira tiriliyan ɗaya da miliyan ɗaya domin cike gibin da masana’antar ke fuskanta, wannan ƙari ne kan tiriliyan huɗu.