
Wasu masu ruwa da tsaki a jam’iyyar PDP a jihar Nasarawa sun yi watsi da amincewar ‘yan takarar da aka ayyana a mukamai daban-daban da za a zaba a jihar gabanin zaben shekarar 2027.
Hakan ya biyo bayan zargin daukar wani dan takara na musamman a matsayin dan takarar jam’iyyar na zaben gwamna a jihar.
Masu ruwa da tsakin da suka kira kan su Concerned PDP Stakeholders Forum, karkashin jagorancin shugabanta Jibrin Idris-Ibrahim sun nuna rashin jin dadinsu kan lamarin yayin ganawa da manema labarai a garin Lafia na jihar Nasarawa a ranar Talata.
Idris-Ibrahim ya bayyana matakin da ake zargin jam’iyyar ta dauka a matsayin wanda bai dace ba, kuma ba tsari ne na dimokradiyya ba. Ya kuma kara da cewa, yin hakan na iya yin barazana ga hadin kan jam’iyyar cikin gida a jihar.
Shugaban ya kuma bukaci kwamitin ayyuka na jam’iyyar na Jiha da su yi watsi da duk wani yunkuri na hakan tare da jaddada aniyar ta na samar da daidaito ga duk masu neman takara.
