
Jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) ta yi watsi da yunkurin haɗa kai da sauran jam’iyyun adawa domin tunkarar zaɓen 2027, tana mai jaddada cewa ba za ta haɗe da kowace jam’iyya ba.
Shugaban SDP, Shehu Musa Gabam, ya shaida wa BBC cewa tsarin jam’iyyar su ya bambanta, musamman kan batun korar ‘yan jam’iyya.
“A SDP, ba za a kori mutum daga jam’iyya ba sai da amincewar shugabancin ƙasa,” in ji shi.
Wannan mataki na jam’iyyar na zuwa ne yayin da ake ganin tagomashinta na ƙaruwa, sakamakon sauya sheƙar da wasu manyan ‘yan siyasa daga wasu jam’iyyun zuwa cikinta.
Daga cikin sabbin ‘yan jamiyyar har da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, wanda ya yi wa wasu shugabannin adawa tayin dawo wa jam’iyyar SDP.
A makon da ya gabata ne wasu jagororin jam’iyyun adawa ƙarƙashin jagorancin tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, suka bayyana yunkurinsu na ƙulla haɗaka domin kawar da APC a zaɓen 2027.
Duk da haka, Shehu Musa Gabam ya ce fiye da ’yan siyasa 200 sun sauya sheƙa zuwa SDP, sai dai bai bayyana sunayensu ba.