Gwamnatin Tarayya ta gina sansanin Soji Uku a Sokoto

0
102

Gwamnatin tarayya ta gina sansanonin soji uku a sassan gabashin jihar Sokoto domin cigaba da yaki da ‘yan ta’adda.

Karamin ministan tsaron kasar nan Muhammad Bello matawalle ne ya bayyana hakan yayin tattaunawar sa da BBC bayan ya kai ziyara wasu yankunan gabashin Sokoto.

Matawalle ya ce an kuma samar da duk abubuwan da ya kamata a sansanonin domin sojojin da za akai su ji dadin gudanar da ayyukan su.

Bello Matawale ya kuma ce ba wai iya jihar Sokoto kawai aka fi maida hankali ba suma sauran jahohin da ke fama da matsalar rashin tsaro ana daukar matakan da suka dace.

Daga bisani karamin ministan tsaro ya kuma gargadi masu bawa ‘yan ta’addan bayanai da su kuka da kan su,domin gwamnati ta tashi tsaye kan su.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here
Captcha verification failed!
CAPTCHA user score failed. Please contact us!