Duka asibitocin sha ka tafi na jihar Kano za su fara aikin awa 24 – KSPHCMB

0
131

Hukumar kula da lafiya a matakin farko ta jihar Kano ta tabbatar da cewa dukkan asibitocin sha ka tafi da ke karkashinta za su fara aiki na tsawon awa 24 nan ba da jimawa ba.

Bashir Sanusi, Daraktan tsare-tsare da bibiya a hukumar ne ya bayyana haka yayin wani taron masu ruwa da tsaki a fannin lafiya da kungiyar Nigeria Health Watch ta shirya.

Taron da ya samu halartar kwamishinan lafiya da sauran masu ruwa da tsaki a fannin, ya yi duba kan yadda za’a inganta ayyukan hukumar lafiyar matakin farkon.

Da yake wa Premier radio karin bayani, Daraktan ya ce tuni shirye-shirye su ka yi nisa domin tabbatar da asibitocin dake karkashin hukumar su na gudanar da aikin awa 24 ba tare da tangarda ba.

Bashir Sanusi ya ce za su tabbatar da samar da ingantaccen yanayi domin ma’aikatan dake aiki a asibitocin karkara.

Kungiyar Nigeria Health Watch ta dauki nauyin tattaunawar da nufin bankado guraben da ake samun tangarda wajen samar da ingantacciyar kulawa ga al’umma domin samar da yadda za a toshe wannan hanya domin ciyar da jihar Kano gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here
Captcha verification failed!
CAPTCHA user score failed. Please contact us!