
Faisal Abdullahi Bila
Hukumar Kidayar Jama’a ta kasa National Population Commission NPC ta ce, ta gamsu da yadda al’umma suka fara fahimtar shirin ta na cin gajiyar yawan mutanen da ake da su a Najeriya.
Kwamishinan hukumar NPC na kasa reshen Kano Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa ne ya bayyana hakan yayin taron bita na yini daya da hukumar ta shiryawa hukumomin gwamnati da kungiyoyin al’uma a Kano a ranar Alhamis.
Dakta Tsanyawa ya ce, daga lokacin da aka fara wayar da kan jama’a tsarin cin gajiyar yawan mutanen da jihar Kano ke da su domin ci gaban kasa, zuwa yanzu kwalliya tana biyan kudin sabulu.
A jawabinsa yayin taron, Daraktan hukumar na Kano, Baba Balarabe Kabir ya ce, idan har iyaye suna yiwa iyalan su kyakkyawan tsarin kula da lafiya da Ilimi da kuma sauran muhimman abubuwan rayuwa, ba za a rika samun yawan al’uma maras amfani ba.
Taron ya samu halartar wasu daga cikin jami’an yada labaran kananan hukumomin Kano da wakilcin majalisar malamai da hukumar Hisbah da kuma sauran hukumomin jihar