
Gwamnatin Jihar Kano ta kammala karɓe gidaje 324 na rukunin Kwankwasiyya, Amana da Bandirawo daga hannun hukumar kula fansho tare da mika su ga hukumar gidaje ta Kano domin gudanarwa da kuma siyarwa ga masu sha’awa.
Wannan mataki ya biyo bayan yanke shawarar gwamna Abba Kabir Yusuf na biyan dukkan bashin da ya rataya kan gidajen, wanda adadinsa ya kai Naira biliyan 4.5.
A sanarwar da mai bawa gwamnan Kano shawara kan harkokin yada labarai Ibrahim Adam ya fitar ya ce, an yi hakan ne domin a samu damar amfana da wanda hakan ke nuna kokarin gwamnan na ganin an kare hakkokin ma’aikatan fansho.
Yayin mika mulkin gidajen, Manajan hukumar Darakta na Hukumar gidaje, ta jihar Kano, Alhaji Abdullahi Rabiu, ya jaddada cewa Hukumar na da kudirin samarwa da kula da gidaje masu inganci domin biyan bukatar yawan jama’ar Kano da ke ƙaruwa.
Haka zalika sanarwar ta kuma bayyana daukar matakin a matsayin yunkurin gwamnatin Kano na ci gaba da nuna nagarta da kuma adalcin salon gwamnatin Injiniya Abba Kabir Yusuf.