Babbar kotun majistare da ke Kaduna ta bayar da umarnin tsare fitaccen mai fafutuka kuma mai sharhi a kafafen sada zumunta, Mahdi Shehu a gidan yari a jihar.
Mahdi ya shiga hannun jami’an hukumar tsaro ta DSS kwanakin baya bayan ya ki janye wasu bidiyoyi da ya wallafa, inda yake zargin cewa shugaba Bola Tinubu ya ba wa Faransa izinin kafa sansanin soji a Arewa.
Zargin da Mahdi ya yi ya zo ne bayan ikirarin shugaban mulkin soji na jamhuriyar Nijar, Abdourahamane Tchiani, cewa Faransa ta kafa sansanin soji a Arewa.
Sai dai mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu da ministan Labarai, Muhammed Idris, sun musanta zarge-zargen, suna masu cewa ba su da tushe balle makama.
A ranar Talata, DSS ta gurfanar da Mahdi a gaban mai shari’a Abubakar Lamido bisa tuhume-tuhume biyu da suka hada da hadin baki, taimakawa da goyon bayan ta’addanci da kuma tayar da hankalin jama’a wanda hakan ya sabawa kundin dokokin laifuka na jihar Kaduna.
Mai shari’a Lamido ya yanke cewa Mahdi zai ci gaba da kasancewa a gidan yari a Kaduna har zuwa ranar 14 ga Janairun 2025, domin ci gaba da sauraron karar.