Ganduje ya dakatar da shirinsa na kafa rundunar Hisbah mai zaman kanta a jihar.
Tsohon gwamnan ya dakatar da shirin ne bayan haramcin gwamnatin jihar ta sanya kan lamarin.
Bayanin hakan na cikin wata sanarwa Baffa Babba Dan-Agundi, na hannun damanaa ya fitar a ranar Talata.
“Matakin ya biyo bayan tattaunawa da Gwamnatin Kano da hukumar tsaro ta DSS, domin tabbatar da zaman lafiya a jihar. ” In ji sanarwar.
An Kuma dauki matakin ne bayan wani taron masu ruwa da tsaki da ya hada wakilai daga kananan hukumomi 44 na jihar a ofishin kamfen na Shugaba Tinubu a Kano.
Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, ya bayyana shirin daukar ma’aikatan Hisbah 12,000 da aka ce gwamnatin jihar ta sallama.
An shirya kungiyar za ta yi aiki a karkashin gidauniyarsa ta Ganduje Foundation.
Gwamnatin jihar ta haramta shirin tare da bayar da umarnin daukar matakan tsaro kan duk wani yunkuri da ya shafi hakan.
