Aminu Abdullahi Ibrahim
Hukumar ilimin bai daya ta jihar Kano (SUBEB) ta ce za ta kwace shagunan kasuwanci wato (Cornorshops) da ke makarantun da dake karkashinta wadanda basa biyan kudin haya.
Shugaban hukumar Yusuf Kabir, ne ya bayyana haka a headkwatar hukumar ranar Laraba.
Yusuf Kabir, ya bukaci wadanda ake bi bashin kudin hayar daga shekarar 2019 zuwa 2023 su hanzarta biya nan da karshen watan Disamba kafin hukumar ta dauki mataki a kansu.
Ya ce Yusuf Kabir, ya nuna damuwa dangane da wadanda suka mallaki kantuna fiye da shekaru ashirin amma basa biyan kudin haya.
Ya ce da kudin da suke biya ne makarantun suke gudanar da kananan gyare-gyare da sauran harkokin gudanarwa.
Shugaban hukumar ta SUBEB, ya kuma tabbatar da cewa dokar da gwamnati ta kafa na hana yin ginin kasuwanci a harabobin makarantu.
Ya ce hukumar a shirye take ta dauki matakin da ya kamata akan duk wanda aka samu da rashin bin dokar.