
Shugaba Tinubu ya sauka a Kano a filin Jirgin Saman Malam Aminu Kano da misalin karfe 3 da minti hamsin da daya na yammacin yau Juma’a domin soma ta’aziyyar.
Shugaban ya samu tarbar ta musamman daga gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf da manyan jami’an gwamnatin jihar da jiga-jigan jam’iyyar APC.
Tinubu ya samu rakiyar Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Barau Jibrin, da wasu cikin yan majalisun dattawa da kuma na wakilai.
Ga yadda ziyarar ta kasance cikin hotuna


shugaba Tinubu


