
Kungiyar Young Nigerian Voices, wacce ke fafutukar wayar da kan matasa da ba su dama a harkokin siyasa da mulki, ta yi kira ga matasa da su maida hankali kan inganta rayuwarsu da rayuwar al’umma gaba ɗaya.
Shugaban kungiyar, Chuku Emeka Nwajiuba, wanda kuma shi ne tsohon karamin ministan ilimi a gwamnatin Buhari, ya bayyana haka yayin ganawa da manema labarai kan ayyukan da kungiyar ke gudanarwa a fadin ƙasar.
Nwajiuba ya ce babban burin kungiyar shi ne wayar da kan matasa, ƙarfafa su da basira, da kuma cusa kyawawan dabi’u da kishin ƙasa domin su zama shugabanni nagari a gaba.
A cewarsa, taimakawa matasa domin su inganta rayuwarsu na da matuƙar muhimmanci ga cigaban ƙasa, kuma hakan ne gabar da kungiyar ta sa gaba.
Ya kuma bayyana cewa a watan azumin Ramadan da ya gabata, kungiyar ta gudanar da rabon kayan abinci ga al’ummar Musulmi a dukkan jihohin Najeriya domin tallafa musu a lokacin ibada.
Young Nigerian Voices na ci gaba da jan hankalin matasa da su kasance masu kishin kasa, tsayawa da gaskiya da kuma kaunar juna domin samar da Najeriya mai inganci.