
Majalisar Dokokin Jihar Kano ta musanta rahoton da ake yadawa na cewar za ta binciki Shugabar Karamar Hukumar Tudun Wada, Hajiya Sa’adatu Yusha’u bisa zargin ta da badakalar filaye.
A wata sanarwa da Babban Sakataren Yada Labaran Kakakin Majalisar Kamal Sani Shawai ya fitar ta ce, Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar, Hoanorabul Lawan Husaini Dala, bai tattauna da kowace kafar yada labarai kan batun ba a jihar.
Da yake yiwa Premier Radio karin bayni, sakataren yada labara Shawai ,ya rawaito shugaban masu rinjayen Lawan husaini Dala yana cewa, a matsayin sa na zababbe yana da hurumin karbar korafe-korafen al’umma domin isar dashi ga majalisr amma bai yi hira da kowane manemin labarai ba.
Majalisar ta kuma bukaci dukkan kafafen yada labaran da suka wallafa ko karanta kagaggen labarin da su gaggauta janye su tare bawa majalisar hakuri a rubuce cikin mako guda ko su fuskanci hukunci a kotu.
Wakilin mu na majalisar dokokin ta kano Kamal Umar Kurna ya rawaito cewa a jiya alhamis ne wata kungiya mai rajin kare hakkin Dan Adam ta mikawa majalisar ta hannun shugaban masu rinjayen Lawan Husaini Dala koken zargin da take yiwa Shugabar karamar hukumar ta Tudun Wada Hajiya Sa’adatu Yusha’u bisa na badakalar gonaki da filayen al’umma inda daga baya kungiyar ta sanar da cewar majalisar ta bakin shugaban rinjayen tayi alkawarin bincikar shugabar, lamarin da majalisar ta musanta.
