

Mutane goma sha uku ne suka rasa rayukansu sakamakon harin da wasu da ake zargin ƴan bindiga ne suka kai a ƙaramar hukumar Mariga ta a daren Talata.
Shaidu sun ce ƴan bindigar sun shiga ƙauyukan ne a kan babura kimanin 150 ɗauke da makamai, inda suka buɗe wuta ba tare da kakkautawa ba, wanda hakan ya haifar da mutuwar mutane 13 da kuma jikkatar wasu da dama.
Rahotanni sun nuna cewa coikin wadanda suka rasa rayuwa kansu akwai jami’an ƴan sa-kai guda uku da kuma wani jami’in ƴansanda da ke bakin aiki a yankin.
Manoma da dama a yankunan sun daina zuwa gonaki saboda fargabar kai musu harin da yan bindiga keyi.