
Ƙungiyoyin Musulmi a Najeriya sun buƙaci mahukunta su saki jagoran al’ummar Falasɗinawa mazauna Najeriya da aka kama tare da tsare shi.
Dattijon mai suna Ramzy Abu Ibrahim wanda ke jagorantar Falasɗinawa mazauna Najeriya ya shafe sama da shekaru 30 a Najeriya.
Da yake yiwa manema labarai Jawabi a Jihar Kwara, jagoran guda daga cikin ƙugiyoyin Musulmin mai suna Al-Harakatul-Islamiyyah Malam Abdur-Razzaq Abdulwahab Al-Ameen Aladodo, ya zargi Isra’ila da hannu a kamen shugaban.
A cewar Ameer na ƙungiyar har yanzu mahukuntan Najeriya basu bada wani cikakken bayani kan dalilin kamen mutumin wanda bai take wata doka ba.
Ya kuma ƙara da cewa Falasɗinawa na zaune lafiya da al’ummar Najeriya don haka take haƙƙinsu ne idan har aka kama jagoransu da bai aikata laifin komai ba.
Malam Abdulrazzak ya kuma ce matuƙar gwamnati bata saki shugaban ba, ba shakka hakan ka iya harzuƙa al’ummar Musulmi da ke Najeriya.