Rundunar yansandan jihar Kano ta ce ta yi nasarar kama wasu da take zargin yanbindiga ne masu satar mutane domin kudin fansa.
Rundunar yan sandan ta ce ta kama mutuman guda biyu ne a ranar Asabar din data gabata a yankin karamar hukumar Shanono bayan samun bayanan sirri.
Kakakin rundunar yan sandan Kano, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, ya yan bindigar sun shigo ne daga jihar Katsina da ke makota da jihar Kano.
Wannan na zuwa bayan da mazauna yankin ƙaramar hukumar Shanono suka koka game da yadda yan bindigar masu satar mutane domin neman kudin fansa suka addabe su.
Ya ƙara da cewa mutanen biyu suna hannun rundunar ƴansandan jihar Kano kuma an a faɗaɗa bincike.
Ya kuma tabbatar da cewa rundunar Kano ta ƙara baza jami’an tsaro domin daƙile matsalar ƴanbindigar.
SP Kiyawa ya ce an girke jami’an tsaro a dajin Ɗansoshiya kan iyakar Kano da jihar Katsina da kuma da ƙananan hukumomin Rogo da kuma Shanono.
Har wa yau a sake baza jami’an tsaro a kan iyakar Kano da Kaduna musamman a dajin Falgore.
Daga bisani kwamishinan yan sandan Kano Ibrahim Adamu Bakori yayi kira ga al’umma dasu ci gaba da sanya idanu tare da bada rahotanni sirri ga duk wata bakuwar fuska da basu amunce da ita ba.
