
Akalla sojoji 50 ne suka rasa rayukansu a wani mummunan hari da wasu ’yan bindiga suka kai kan wani sansanin soji da ke arewacin Burkina Faso, kamar yadda majiyoyi suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na Associated Press (AP).
Harin ya auku ne a ranar Litinin da ta gabata a sansanin Dargo da ke lardin Boulsa, inda ake zargin kungiyar Jama’at Nasr al-Islam wal-Muslimin (JNIM), wata kungiya da ke da alaka da Al-Qa’ida, da kai hari.
Wani shugaban al’umma da wani mazaunin yankin, wadanda suka nemi a boye sunayensu saboda tsoron ramuwar gayya daga jami’an tsaro, sun ce ’yan bindigar da yawansu ya kai kusan 100 ne suka afka wa sansanin, inda suka kashe sojoji da dama, sannan suka kona sansanin tare da yin awon gaba da kayayyaki.
Majiyoyin sun ce har yanzu ba a ga wani rahoton hukumomi ba game da yawan asarar rayuka ko barnar da aka yi.
Gwamnatin mulkin soja ta Burkina Faso ba ta fitar da wata sanarwa ba dangane da harin.