Ƙungiyar Likitocin masu neman kwarewa ta bai wa gwamnatin tarayya wa’adin kwanaki talatin domin warware matsalolin da suka shafi walwalar ma’aikatanta da wasu batutuwan aiki ko ta tsunduma yajin aiki.
Ƙungiyar ta fitar da wannan sanarwa ne bayan babban taronta na shekara na 45 da aka gudanar a Jihar Katsina, inda ta gargadi gwamnati cewa za ta iya tsunduma cikin yajin aiki idan ba a ɗauki mataki ba cikin wa’adin da aka bayar.
Daga cikin manyan buƙatun Ƙungiyar har da biyan bashin kuɗaɗen ƙarin girma na shekaru da suka wuce, sakin sabon jadawalin alawus ɗin ƙwararru, maido da likitoci biyar da aka sallama daga Asibitin Koyarwa na Lokoja, da kuma kammala duba tsarin sabon albashi na CONMESS.
Ƙungiyar ta kuma nuna damuwa kan tsawon sa’o’in aiki da likitoci ke yi, tare da umartar mambobinta da su daina yin aiki fiye da sa’o’i ashirin da huɗu a jere daga ranar ɗaya ga watan Oktoba.