Adamu Atiku Abubakar, ɗan tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi murabus daga muƙaminsa na Kwamishinan Ayyuka da Makamashi na Jihar Adamawa.
A cikin wasiƙar murabus ɗinsa mai kwanan wata 2 ga Maris, 2026, wadda ya aika wa Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri, Adamu ya bayyana cewa ya ɗauki matakin ne bayan “zurfin tunani da yin nazari.”
Adamu ya bayyana cewa kasancewarsa a muƙamin wata babbar dama ce da ya ɗauka a matsayin karramawa. Ya gode wa gwamnan bisa ba shi damar yin aiki a ƙarƙashin jagorancinsa tare da bayar da gudunmawa wajen bunƙasa jihar.
Haka kuma, ya gode wa al’ummar Jihar Adamawa bisa goyon baya da amincewar da suka nuna masa a tsawon lokacin da yake kan muƙami. Ya ce yanayin aiki mai kyau da gwamnan ya samar ya ba shi damar gudanar da aikinsa cikin ƙwazo da jajircewa.
A ƙarshe, ya yi addu’ar Allah Ya ba gwamnan ƙarfi da shiriya domin ci gaba da yi wa jihar hidima.
Rahotanni sun nuna cewa Adamu bai sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC ba. Kuma an lura cewa bai halarci taron kwamishinoni 22 da suka raka Gwamna Fintiri domin sanar da ficewarsu daga jam’iyyar PDP zuwa APC a ranar 27 ga Fabrairu, 2026 ba.
