Rundunar ‘Yan Sanda ta Babban Birnin Tarayya (FCT) ta cafke mutum 19 da ake zargi ‘yan kungiyar asiri ne, bayan sun yi artabu da jami’an tsaro a unguwar Bakassi Yimitu da ke yankin Apo-Waru a Abuja.
A cewar rundunar, an yi musayar wuta tsakanin jami’an tsaro da wadanda ake zargin, inda ɗan sanda guda da wani ɗan banga suka jikkata kuma aka garzaya da su asibiti domin samun kulawar likita.
Wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Josephine Adeh, ta fitar a ranar Juma’a a Abuja ta bayyana cewa, Kwamishinan ‘Yan Sanda na FCT, CP Ajao Adewale, ya jagoranci hadin gwiwar jami’an tsaro da ‘yan banga da mafarauta wajen gudanar da sintiri na dakile aikata laifi a ranar Laraba, 24 ga Yuli, 2025, a unguwar Bakassi Yimitu bisa korafe-korafen da mazauna yankin ke yi kan ayyukan ‘yan kungiyar asiri.
Sanarwar ta ce Lokacin da jami’an suka isa wajen, sun tarar da taron wasu da ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne da suka addabi yankin. Da suka hango jami’an tsaro, sai suka fara bude musu wuta. An yi musayar wuta, wanda ya kai ga cafke mutane 19 da aka kulle a ofishin ‘yan sanda na Waru, yayin da wasu suka tsere da raunuka daban-daban.
Kwamishinan ‘Yan Sanda ya bayyana cewa rundunar zata cigaba da kokarin kamo sauran wadanda suka tsere domin fuskantar hukunci.
