
Tsohon gwamnan jihar Kano Rabiu Musa Kwankwaso da jami’iyyar NNPP na duba yiwuwar kawance da jam’iyya APC mai mulki ko kuma kawancen ‘yan adawa karkashin jagorancin Atiku Abubakar kafin babban zaben 2027.
Wata majiya ta bayyana wa jaridar Punch da wuya jamiyyar ta sake tsayawa takara ita kadai kamar yadda ta yi a 2023.
Kakakin jam’iyyar NNPP na kasa, Ladipo Johnson, ya tabbatar da cewa suna tattaunawa da wasu bangarori, amma har yanzu ba su yanke shawarar karshe ba tukunna.
“Muna sa ido kan yadda gwamnati ke tafiya, kuma za mu bayyana matsayarmu zuwa 29 ga watan Mayu lokacin da gwamnatin Bola Tinubu ke cika shekaru biyu cif.”
A cewarsa, akwai zabi uku da ke gabansu na ci gaba da zama a NNPP kamar yadda suke a yanzu ko kuma shiga kawance da su Atiku Abubakar da sauran yan siyasa, ko kuma hadewa da jam’iyyar APC mai mulki.
Ya kara da cewa nan ba da jimawa ba za su bayyana matsayinsu ga magoya baya.