Sanata mai wakiltar mazaɓar Bauchi ta Kudu, Sanata Shehu Buba Umar ya ƙaryata labarin da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke cewa Majalisar dattawa ta amince da ƙirƙiro sabbin jihohi guda 12.
Da yake ganawa da ƴan jarida a Bauchi ranar Asabar Buba ya fayyace cewa, a halin da ake ciki dai majalisar ta kafa kwamitocin jin ra’ayin jama’a daga sassa daban-daban har guda shida na ƙasar nan.
An kafa kwamitinne duba yadda za yi kwaskwarima ga kundin tsarin mulki na 1999 tare da neman ƙirƙiro sabbin jihohi da ƙananan hukumomi.
Ya tabbatar da cewar a halin yanzu majalisar dattawa ko karɓar rahoton kwamitocin jin ra’ayoyin jama’a ba ta yi ba, balle ta zauna ta tantance ta duba wuraren da suka dace a amince da samar da sabbin jihohi ko ƙananan hukumomi a cikinsu.
