Aminu Abdullahi Ibrahim
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya ce nan ba da jimawa ba gwamnatin sa zata samar da hukumar kula da masu bukata ta musamman.
Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake sanar da daukar wata mai lalurar gani Hassana Nazifi Shehu Minjibir aiki.
Gwamnan ya bata aikin ne yayin taron tallafawa mata da dabbobi da jari domin yin kiwo don dogaro da kansu ranar Talata da aka yi a unguwar Mariri.
Matar dai ta kammala karatun Degree a jami’ar Bayero inda ta karanci bangaren ilimin masu bukata ta musamman.
Abba Kabir Yusuf, ya nuna jin dadin sa bisa jajircewarta wajen ganin ta cika burinta duk da kalubalan da take da shi na nakasa.
Gwamna Abba Kabir ya kara da cewa baya ga bata aiki yayi alkawarin nada ta cikin hukumar kula da masu bukata ta musamman wadda gwamnatin sa zata kafa nan bada jimawa ba.
Ya kuma umarci ofishin shugaban maaikata da a gaggauta bata takardar aiki ba tare da bata lokaci ba.