
Ahmad Hamisu Gwale
Hukumar Kwastam ta sanar jami’anta sun kama tabar wiwi mai darajar naira miliyan 48.5 da wasu kayan da aka haramta na naira miliyan 220 a Jihar Kaduna.
Kwamandan hukumar ya ce an kama kayayyakin ne a ranar 21 ga Agusta, 2025, a wurare daban-daban a jihar.
Ya ce jami’an sashen bisa ingattatun bayanan da suka samu ne suka tsayar da mota a Zaria kan babbar hanyar zuwa Kano inda suka yi nasarar kama tabar wiwi ɗin da sauran kayan da aka haramta.
Mai magana da yawun hukumar kwastam ya ce an miƙa wanda ake zargin da kayan ga jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, don ci gaba da bincike da gurfanarwa a gaban shari’a bisa tsarin haɗin gwiwar hukumomi.