
Wasu da ake zargin ’yan kungiyar Boko Haram ne sun kai hari kauyen Kopl da ke karamar hukumar Chibok, sun kuma hallak akalla mutane bakwai (7) tare da jikkata wasu da dama.
Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Litinin, yayin da mazauna kauyen ke gudanar da zaman makoki na iyalan su da suka rasa rayukansu a wani hari da aka kai a baya.
Shugaban karamar hukumar Chibok, Modu Mustapha, ya tabbatar da faruwar harin. Ya kuma ce, wadanda suka jikkata an garzaya da su zuwa babban asibitin Mubi a jihar Adamawa domin samun kulawar gaggawa daga likitoci.
“Harin ya haifar da rudani da karin hasarar rayuka, wanda hakan ya hana gudanar da jana’izar mutanen da aka kashe a baya, kamar yadda aka tsara a yau Talata,” in ji Mustapha.
Sabon harin ya zo ne sa’o’i kadan bayan fashewar wani abu da ya afku a hanyar Gamboru Ngala zuwa Kala Balge wanda ya yi sanadin mutuwar matafiya 12, a cikin jihar ta Borno.
Hare-haren ’yan bindiga a yankin Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma na ƙara ta’azzara a ‘yan kwanakin nan lamarin da ke kara haddasa tsoro da fargaba a zukatan mazauna yankunan.
Masu sharhi na cewa hauhawar ayyukan ta’addanci a yankin na bukatar tsauraran matakan tsaro da hadin gwiwa tsakanin hukumomi da al’umma domin dakile hare-haren da ke ci gaba da janyo asarar rayuka da dukiyoyi.