
Fadar shugaban kasa ta mayar da martanin kan umarnin Kotun Amurka da na a fitar da bayanai kan Tinubu da zargin badakalar miyagun kwayoyi.
A cikin wata sanarwa da Bayo Onanuga Babban Mai Magana da Yawun shugaban kasa ya fitar a ranar Lahadi, ya ce, wannan batu ba sabon abu ne.
“Babu wani sabon abu da za a bayyana. Domin rahoton sirri na hukumomin FBI da DEA na Amurka na nan a bayyane sama da shekara kuma babu ya zarge shi aikata laifi. Sai dai duk da haka, lauyoyinu na nazarin hukuncin.” in ji shi.
A ranar Talata ne wata kotu a Amurka ta umurci Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta ƙasar (FBI) da ta fitar da bayanan sirri da aka samu kan Shugaba Bola Tinubu a lokacin wani binciken badaƙalar miyagun ƙwayoyi da gwamnatin ƙasar ta yi a shekarun 1990.
Jaridar Premium Times ta ruwaito Alƙalin kotun, Beryl Howell wanda ya ba da umarnin a ranar Talata, yana mai cewa babu ma’ana a rufe bayanan ba tare da an bayyana wa jama’a ba.
A watan Yunin 2023 ce wani Ba’Amurke, Aaron Greenspan, a ƙarƙashin dokar ’yancin fitar da bayanai (FOAI) ya miƙa buƙatar a ofishin zartarwa na lauyoyin Amurka, da Hukumar FBI da Hukumar Yaƙi da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (DEA) da kuma Hukumar Leƙen Asiri ta (CIA).
Wasu bayanai na cewa, a shekarar 1993 ce Tinubu ya sarayar da kimanin Dala 460,000 ga gwamnatin Amurka bayan mahukunta sun alaƙanta kuɗin da fataucin miyagun ƙwayoyi.
Ana iya tuna cewa, wannan hujja ta rashin cancantar tsayawa takara manyan ’yan adawar Shugaba Tinubu — Atiku Abubakar da Peter Obi — suka gabatar a yayin ƙorafin zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
Sai dai kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓen ta yi watsi da ita tana mai tabbatar da nasarar Tinubu a babban zaɓen ƙasar ma 2023.