Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu, wanda ake zargi da laifukan cin hanci da rashawa, ya gabatar da neman afuwa ga Shugaban kasar Aizik Hesko.
Netanyahu na fuskantar shari’o’i guda uku daban-daban na cin hanci da rashawa da aka shigar tun a shekarar 2019, waɗanda suka ƙunshi zarge-zargen cin hanci, zamba, da kuma cin amana, yayin yake ci gaba da musanta aikata laifukan da ake tuhumarsa a kai ba.
Buƙatar Benjamin Netanyahu ta zo ne dai dai lokacin da Shugaban Amurka Donald Trump ke matsa wa lamba kan ya yafe wa Firaministan.
Haka zalika, shugaban kasar ya kuma sami wasiƙa daga Donald Trump a farkon watan Nuwamba, yana roƙonsa da ya yi la’akari da buƙatar afuwar Benjamin Netanyahu.
A watan Nuwamban 2024, kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC, ta bayar da sammacin kama Netanyahu da kuma tsohon ministan tsaron Isra’ila, bisa zargin laifukan yaƙi da cin zarafin bil’adama a zirin Gaza.
Netanyahu shi ne firaminista ɗaya tilo da ke kan mulki a tarihin Isra’ila wanda ya fuskanci shari’a, bayan an tuhume shi da zamba, cin amana da kuma karbar cin hanci a mabanbantan shari’o’i
