
Hukumomi a Kamaru sun haramta duk wata zanga-zanga a kan titunan babban birnin kasuwancin ƙasar har sai an rantsar da sabon shugaban ƙasar.
Matakin ya zo ne bayan wasu manyan zanga-zanga da suka ɓarke a birnin mai tashar jiragen ruwa da kuma a wasu yankunan kasar kan zargin kokarin murde sakamakon zaben da shugaban ‘yan adawa ya tasamma nasara.
Tun bayan zaben aka samu hargitsi a lardi na biyar na Douala inda cincirindon mutane suka taru a wajen ofisoshin hukumar zaɓe ta ElCAM sanadin zarge-zargen cusa ƙuri’u a akwatunan zaɓe.
Rahotanni sun ce, mazaunan yankin da yawa ne suka taru suna yin Allah-wadai da kura-kuren da aka samu da kuma neman a tabbatar da gaskiya a akwatunan da aka jefa ƙuri’u.
Ƙungiyoyin fararen hula da masu sa ido a zaɓen sun yi tir da yunƙurin a matsayin wani farmaki kan ‘yancin gudanar da taruka.
A lokaci guda kuma, ɗan takarar adawa Issa Tchiroma Bakari, ya fitar da wani jawabi ta bidiyo inda ya buƙaci masu sa ido a zaɓen su hana jirkita sakamakon zaɓen kuma su dage wajen kare muradin al’ummar ƙasar.