Gwamnan jihar Borno ya ce za su yi hakan ne domin dokar za ta kassara arewa ne ta kuma daukaka arzikin jihar Legas kadai
Farfesa Babagana Umara Zulum ya kuma ce za su hada kan ‘yan majalisar dokoki ta kasa daga arewa domin yakar sabbbin dokokin karin haraji.
Gwamnan ya ce bai kamata gwamnati ta nuna bukatar ‘yan majalisar ta kasa su hanzarta amincewa da dokar ba, wacce a cewarsa za ta kassara arewa ne ta daukaka tattalin arzikin jihar Legas kadai.
Sannan ya ce, abin da ke daure musu kai shi ne yadda Tinubu ke son ‘yan majalisar gaggauta amince wa da ita da kuma azarɓaɓin ganin kudirin dokar ya soma aiki nan ba da jimawa ba.
“Akwai kudirori a baya da suka shafe shekaru ana jayayya a kai, me ya sa a wannan lokaci ba za a natsu a fahimci kudirin ba kafin ta zama doka.
“Ko yankunan kudancin Najeriya akwai shiyoyyi irinsu Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas da Kudu maso Yamma da dukka ba wai murna suke da wannan doka ba.”
Zulum ya tuna wa shugaban kasa cewa arewa ce ta ba shi kashi 60 cikin 100 na kuri’un da ya samu.