
Tsohon ɗan takarar kujerar sanatan Kano ta Tsakiya Alhaji Abdulsalam Abdulkarim Zaura ya ce, za su yi duk mai yiwuwa domin ganin sun sulhunta tsakanin Rabiu Musa Kwankwaso da Abdullahi Umar Ganduje da kuma Ibrahim Shekarau.
Zaura ya ce, haɗin kan manyan jagororin zai taimaka wajen gyara siyasar jihar, tare da samar da ci gaba ta yadda jihar za ta yi gogayya da jihar Legas da wasu jihohin da suka ci gaba.
“Irin adawar siyasa da ake yi a Kano ba ta da amfani, kamata mu fifita ci gaban Kano sama da son ranmu. a shirye nake in shige gaba wajen samar da maslaha tsakanin Kwankwaso da Ganduje da Shekarau.” Inji shi.
Ya kuma ce, da zarar an samu wannan nasarar, Legas da sauran jihohi sai sun yi koyi da Kano wajen siyasa ta hankali da ci gaba.
A baya Abdulmumin Jibrin Kofa da Murtala Sule Garo da Baffa Babba Danagundi duk sun bayyana irin buƙatar a lokuta daban-daban.
