Ministan Tsaro Abubakar Badaru, ya nemi gwamnatin tarayya ta kara yawan kudin da aka warewa bangaren tsaro da yawan Karin kaso a kasafin kudin 2025
Hakan zai ba su damar sayo karin motocin yaki 50 a cikin kasafin kudin 2025 don kawo karshen yan ta’addan da suka addabi kasar nan.
Ministan ya bayyana hakan ne ta hannu Karamin Ministan Tsaro Bello Matawalle wanda ya wakilce shi a zaman da majalisar ta yi na kare kasafin kudi a majalisar wakilai.
“Jimillar biliyan N50.44 da aka ware wa Ma’aikatar Tsaro a kudirin kasafin kudin 2025 bai wadatar ba wajen magance matsalar tsaron dake ci gaba da ciwa ‘yan kasa tuwo a kwarya
“Idan har akwai kayan aikin da suka dace, to kuwa yana da tabbacin jami’an tsaron kasar nan za su iya kawo karshen ‘yan ta’addan kasar nan cikin watanni biyu.”
Inji Karamin Ministan ya kuma ce, a yanzu jami’an tsaron suna da motocin yakin guda 20 ne kacal, a don haka ne suka bukaci karin motocin da jami’an tsaro za su kutsa kai cikin dazukan da bayanan sirri suka bayyana matattara ce ta yan taaddan don tarwatsa su.
A don haka ne ya kuma nemi goyon bayan kwamitin tsaro na majalisar ya amince da kari